Mista Zhong ya fadi hakan ne, a 'yan kwanakin baya, yayin da yake zantawa da manema labaru a birnin Yaounde, hedkwatar kasar Kamaru. Kaza lika, ya gabatar da ra'ayinsa game da batutuwan da ke haifar da kalubale game da aikin shimfida zaman lafiya da tsaro a Afrika, kamar batun Sudan ta Kudu, da rikicin Somaliya, da na kasar Mali da kuma kasar Kongo (kinshasa).
Wakilin na Sin ya kuma sake nanata cewa, kamata ya yi al'ummar Afrika ta warware batutuwan da suke shafe bisa dabaru irin nata. Yayin da Sin ke ganin dacewar amfani da kungiyar AU, da sauran kungiyoyin shiyya-shiyya da kasashen da rikicin ya shafa kansu don warware matsalolin Afrika. (Bako)