Kungiyar 'yan kasuwa masu zaman kansu na kasashen Sin da Afirka, Asusun taimakawa zaman takewa(ta UNAIDS) da kuma jami'ar kimiyya da fasaha ta Beijing ne suka kira bikin cikin hadin gwiwa, domin amsa kiran da MDD ta yi wa matasan kasa da kasa, da su kara sanin illar cutar kanjamau, da kuma taimakawa kasashen Afirka wajen yin rigakafi da kuma hana yaduwar cutar.
Mataimakin babban magatakardan MDD, kana babban darektan hukumar UNAIDS Michel Sidibe ya yi jawabi a yayin bikin cewa, ya kamata matasan kasa da kasa su hada kai domin kafa wani dandalin kawar da cutar kanjamau tsakanin matasa.
Bugu da kari, a yayin da ya ke jawabi, babban sakataren kungiyar 'yan kasuwa masu zaman kansu na Sin da Afirka Wang Xiaoyong ya ce, kasar Sin na taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen kamuwa da cutar kanjamau, kawar da nuna bambanci ga wadanda suka kamu da cutar, da kuma kawo karshen mutuwar mutane sakamakon kamuwa da cutar, dangane da haka, kungiyar za ta karfafa hadin gwiwa da hukumar UNAIDS kan taimaka wa kasashen Afirka guda takwas wadanda suka fi fama da cutar, da kuma kara zuba jari cikin shirin hukumar, ta yadda za a iya ciyar da aikin yin rigakafi da kuma hana yaduwar cutar kanjamau a Afirka gaba. (Maryam)