Kasar Afrika ta Kudu ta kai ga wani mataki, na kusa da samar da wata ingatacciyar allura, mai gagarumin tasirin murkushe kwayar cutar nan ta AIDS mai karya garkuwar jikin bil Adama.
Ministan lafiya, na kasar Africa ta Kudu, Aaron Motsoaledi, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, bayan da masanan kimiyya suka gano wasu nau'o'in kwayoyin halitta, wadanda ke da karfin murkushewa tare da hallaka wasu jerin nau'o'in kwayoyin cutar nan mai karya garkuwar jikin bil Adama watau AIDS.
Tun farko dai, a ranar ta Litinin, cibiyar binciken cutar AIDS ta Afrika ta Kudu CAPRISA ta bayar da rahoton gano yadda jikin wata mata dake Kwa Zulu-Natal mai dauke da cutar AIDS, ya samar da sojojin kariyar jiki, da ake kira sojoji masu bayar da babbar kariya.
Rahoton ya ruwaito cewar, matar na samun sauki, a yayin da take ci gaba da amfani da magungunan cutar ta AIDS, tare da ci gaba da halartar cibiyar lafiya ta CAPRIS a kai a kai.
Kamar dai yadda cibiyar hulda da samar da bayanai ta Afrika ta Kudu ta bayyana, wannan bincike na hadin gwiwa ne, daga bangaren cibiyar binciken cutar AIDS ta CAPRISA tare da masanan kimiyya na jami'ar Wits, da cibiyar binciken cuta mai yaduwa ta kasar dake Johannesburg, da kuma Jami'ar Kwa Zulu-Natal, gami da jami'ar garin Cape Town da masana kimiyya na Amurka. (Suwaiba)