in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban MDD ya bukaci karin kokari domin a samu kau da cutar Sida a duniya
2013-06-11 17:06:12 cri
Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon a jiya Litinin 10 ga wata, ya yi kira ga hukumomin kasa da kasa da su matsa lamba tare da bada himma domin cimma burin ganin an kau da cutar sida a duniya baki daya. Ya ce ya kamata a matsa daga zuba miliyoyin kudade wajen magance cututtuka zuwa ga zuba miliyoyin kudade wajen bada damar da al'ummomi za su rayu.

Mr. Ban wanda yake magana a lokacin da majalisar ta yi wani taro domin nazari a kan cigaban da aka samu a duniya wajen yaki da cutar ta sida, yace sakamakon da aka samu a wannan aiki zai gina ayyukan kiwon lafiya mai karko da kuma wadata ga bukatun al'umma baki daya.

Ya lura cewar taron da suka yi ya zo a daidai da kusan rabin lokacin da Majalisar ta tsaya a shekara ta 2011 game da cutar ta sida kuma an samu cigaba mai armashi a cikin shirin, kamar yadda ya lissafa cigaban shirin zuwa yau adadin yaduwar ya daidaita kuma yawan sabbin kamu yayi baya a kasashe fiye da 56 a duniya. A bisa kididigar da ya ba bayar ya nuna cewar cutar ta rage yaduwa da kashi daya cikin biyar tun daga shekarar ta 2001, sannan magunguna sana kaiwa ga fiye da rabin mutane masu fama da cutar a kasashen marasa karfi sosai.

Babban magatakardar yayi bayani ga mambobin majalisar 193 cewa, ana samar da sabuwar hanya da za'a samu nasarar ganin an cimma kudurin tabbatar da duniyar da ba ta fama da wannan lalurar. Yana mai cewa, gaba daya za'a iya samun nasara muradun karni wanda shi ne zai dakatar tare da hana yaduwar cutar ta sida nan da shekara ta 2015. Sai dai fa inji shi, sai an kara himma ga kowace kasa da al'ummominsu, kuma ana bukatar karin kudi domin ganin hakan ya tabbata.

Har ila yau Mr. Ban yace mata da yara har yanzu suna cikin hadarin kamuwa da wannan cuta, yana mai bayani da cewa a cikin ko wane minti daya a kalla matashiyar mace daya tana kamuwa da wannan cuta, bugu da kari samar da magungunan cutar ga yara kanana har yanzu yana da rauni domin kusan kashi daya bisa uku ne na yaran da suke fama da cutar suke samun maganin da suke bukata.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China