Daliban dai sun gudanar da wasu al'amura da suka hada da ziyarce-ziyarce a wasu manyan makarantun kasar ta Kenya, karkashin shirin da a kaiwa lakabi da "kokarin matasa, burin kasar Sin, da zumuncin kasashen Afirka".
Rahotanni dai sun ce daliban sun shafe makwanni 2 suka gudanar da wannan hidima, sun kuma cimma nasara mai yawa, a fagen ciyar da shawarwari tsakanin matasan kasar Sin da na nahiyar Afirka gaba.
Daliban dai sun halarci nahiyar Afirka ne karkashin kudurorin hukumomin ba da ilmi da taimaka wa talakawa, da na kiyaye namun daji, da kuma dandalin tattaunawa tsakanin matasan Sin da kasashen nahiyar Afirka. (Maryam)