A ranar Litinin, magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya baiyana cewa, MDD ta kaddamar da wani dandalin internet don baiwa matasan duk duniya damar baiyana ra'ayoyinsu ga MDD.
Dandalin na Ahmad Alhendawi, wanda shi ne na farko irinsa da Mr. Ban ya kaddamar domin matasa, an kuduri yinsa ne a farkon shekarar nan kuma aka kaddamar ranar Litini a matsayin dandalin matasa na internet.
Magatakardan ya ci gaba da cewa, Alhendawi yana aiki tare da cibiyar bunkasa harkokin matasa ta MDD domin a samu hado dukkan sassan MDD waje guda domin matasa, inda kuma za'a mai da hankali kan ayyukan yi da fasaha, shigar da su harkokin siyasa, harkokin jama'a da kare hakkin bil adama, ilmi da kuma fadakarwa kan ilmin jima'i da kiwon lafiya.
Ban ya baiyanawa matasa da yawansu ya kai dubu daya wadanda aka yi shirin tattaunawa na duniya kan MDD tare da su, ta hanyar amfani da bidiyo cewa, 'A zamaninku ne aka samu matasa mafi yawa a duniya.'
Ya ce, yanzu kun samu wata damar yin sadarwa da daukar mataki, to amman akwai kalubale, musamman ma a fuskar karuwar rashin daidaito na 'yanci, koma bayan dama na yin abubuwa, ga kuma barazanar dumamar muhalli da lalacewar muhalli. (Lami)