Najeriya ta cimma wani shirin da zai kawo sauki ga matasan kasar miliyan 15 wajen daukar nauyin kansu da kansu
Tarayyar Najeriya ta gabatar a ranar Talata da wani shirin aiki na shekaru biyar masu zuwa na gwamnatin kasar da zai taimaka wajen kawo sauki ga matasan kasar miliyan goma sha biyar a cikin wani tsarin baiwa matasa wata damar tafiyar da harkokinsu (IYEP). Mashawarcin musamman na shugaba kan baiwa matasa wannan cin gashi, Obinna Adim ya gabatar da wannan shiri a gaban manema labarai a birnin Abuja, bayan wani taro tare da shugaban kungiyar kula da gasar harkokin cinikayya ta daliban manyan makarantun sakandare (SAGE) dake a kasar Najeriya, mista Agwu Amogu.
Mista Adim ya bayyana cewa, ofishinsa ya shigar da tsarin IYEP a matsayin wani jadawalin da zai taimaka ma matasan Najeriya rike makomarsu da kansu. Muna imani cewa wannan dabara da za ta iyar budewa matasa wata hanyar samun gashin kai tasu wajen tafiyar da harkokinsu a cikin shekaru biyar masu zuwa. Haka zalika, hangen makoma da nuna gaskiya kan cimma manufa su ne manyan jigogi na wannan tsari.
A cewarsa SAGE zata iya kasancewa a matsayin hanyar yin cudanya ta fuskar hada kai wajen kirkirowa, ta yadda za'a iya kyautata halin zaman rayuwar matasa cikin yanayin da ya dace. (Maman Ada)