Sakon dai na nuna cewa girgizar kasar mai karfin digiri 7.9 bisa ma'aunin Richter, ta auku ne a Asabar din nan, ta kuma haddasa lalacewar wasu gine-gine. Sai dai kawo yanzu ba a kai ga tantance yawan mutanen da suka rasu, ko wadanda suka jikkata ba.
Baya ga gine-gine da suka lalace, an ce girgizar kasar ta kuma barnata turakun sadarwar wayar tarho dake birnin.
Rahotanni sun bayyana cewa an ji tasirin wannan girgizar kasa a arewa da tsakiyar India, amma babu rahoton rasuwa ko jikkatar mutane. Kaza lika an dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa na karkashin kasa a birnin New Delhin kasar India na dan lokaci. Amma ance yanzu haka an ci gaba da gudanar da sufuri ta layin dogon kamar yadda aka saba.
Baya ga yankin India, an ji tasirin wannan girgizar kasa a Malaysia da Bangladesh, da ma wasu sassan jihar Tibet na nan kasar Sin.(Fatima)