Shugaban kasar Sin Mr Xi Jinping ya gana da shugaban majalisar dattawa ta kasar Pakistan Mian Raza Rabbani da ma shugaban majalisar wakilan kasar Sardar Ayaz Sadiq a ranar talatan nan 21 ga wata a Islamabad babban birnin kasar ta Pakistan.
Yayin ganawar, Mr Xi ya nuna cewa, majalisar dattawa da ta wakilan kasar Pakistan sahihan abokai ne wajen bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Pakistan. Ya kamata hukumomi masu kula da dokoki da shari'a na kasashen biyu sun kara cudanya tsakaninsu don taimaka wajen sa kaimin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangare kuma, Mian Raza Rabbani da Sardar Ayaz Sadiq sun bayyana cewa, bunkasa huldar abokantaka da kasar Sin babban tushe ne na manufar diplomasiyya ta kasar Pakistan, wanda ke samun karbuwa sosai daga jama'arta. Majalisun biyu na fatan kara yin mu'ammala tsakanin majalisun dokokin kasashen biyu don kara fahimtar juna da amincewa da juna. (Amina)