Ya yi wannan kiran ne cikin wata sanarwar da ya sanya ma hannu wanda kafofin watsa labaran Pakistan suka bayyana a gabannin ziyarar aikin da zai kai kasar a gobe litinin.
A cikin sanarwar yace yana sa ran aiki da shugabannin Pakistan a lokacin ziyarar tasa domin samar da hanyoyi hadin gwiwa, da kuma samun ingantaccen cigaba a bangaren bunkasa hanyar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu har ma da hadin gwiwa a sauran bangarori da dama domin daukaka amincin dake tsakanin zuwa wani sabon matsayi.
Pakistan ne zangon shugaban na farko a ziyarsa zuwa kasashen waje a wannan shekarar inda a karshen ziyarar a ranar talata zai tashi zuwa kasar Indonesia domin halartar taron Bandung.
A lokacin ziyarar tasa a Pakistan, shugaba Xi zai gana da Takwaransa Mamnoon Hussain, da firaministan kasar Nawaz Sharif da sauran shugabannin kasar, inda zasu tattauna mai zurfi akan batutuwa da suka shafi hadin gwiwwa da sauran bangarin da suka fi jawo hankalin sassan biyu.(Fatimah Jibril)