in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing zuwa kasar Pakistan
2015-04-20 09:40:59 cri
A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tashi daga nan birnin Beijing zuwa kasar Pakistan, domin gudanar da ziyarar aiki inda zai gana da shugaban kasar ta Pakistan Mamnoon Hussain, da kuma firaministan kasar Mian Muhammad Nawaz Sharif.

Kaza lika shugaba Xi Jinping zai wuce kasar Indonesia bayan ganawar da Shugaba Joko Widodo, zai kuma halarci taron shugabannin Asiya da Afrika, da kuma bikin tunawa da ranar cika shekaru 60 da bude taron Bandung.

Shugaban na Sin dai na tare da uwargidan sa Peng Liyuan, da mamba a hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, kuma shugaban ofishin nazarin manufofin kwamitin tsakiya Wang Huning. Sauran 'yan tawagar tasa sun hada da sakataren sashen sakatariyar kwamitin tsakiya na JKS, kuma direktan ofishin kula da harkokin yau da kullum na kwamitin tsakiya Li Zhanshu. da mamban majalisar gudanarwa ta kasar Yang Jiechi da dai sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China