in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya isa Islamabad domin ziyarar aiki
2015-04-20 16:58:10 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping a litinin din nan da rana ya sauka a birnin Islamabad babban birnin kasar Pakistan a ziyarar sa ta farko zuwa kasar da ke kudancin yankin Asiya.

Pakistan dai itace zangon shi na farko a ziyarar sa zuwa kasashen wajen a wannan shekarar. Jiragen sojin sama guda 8 suka raka Jirgin shugaba Xi lokacin da ya shigo sararin samaniyar Pakistan.

A ziyarar tasa ta yini biyu, shugaba Xi zai gana da takwaran sa Mamnoon Hussain, da firaministan kasar Nawaz Sharif da sauran shugabannin kasar tare da al'ummomin wakilan sassan daban daban domin yin tattaunawa mai zurfi game da dangantakar diplomasiya da kuma musayar ra'ayi.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China