in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron Bandung na da ma'ana sosai, in ji mataimakin ministan harkokin waje na Sin
2015-04-20 20:53:39 cri
A yau Litinin 20 ga wata, aka kira taron ministoci na share fagen taron shugabannin kasashen Asiya da na Afirka da kuma bikin tunawa da cika shekaru 60 da taron Bandung a birnin Jakarta na Indonesiya.

Ministan harkokin waje na kasar ta Indonesiya, Retno Marsudi da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu, Maite Nkoana-Mashabane suka jagoranci taron, yayin da wakilai daga kasashen Asiya da na Afirka kimanin 100 a matsayin ministoci suka halarci taron.

Mataimakin ministan harkokin waje na Sin, Liu Zhenmin ya halarci taron, inda a cikin jawabinsa ya ce, taron Bandung da aka yi yau da shekaru 60 da suka wuce na da ma'ana sosai, wanda ya sa kaimi ga hadin gwiwa da bunkasuwar kasashen Asiya da na Afirka, da kara kwarin gwiwar kasashe masu tasowa wajen neman samun 'yancin kansu, tare da kaddamar da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa da taron kungiyar 'yan ba ruwanmu.Hakan ya sa kaimi ga yin kwaskwarima ga tsarin kasashen duniya.

Bayan haka, Liu ya jaddada cewa, Sin ta taba ba da gudummawarta ga taron Bandung a shekarar 1955. A yau kuma, wato ranar da aka gudanar da taron bayan shekaru 60, Sin na fatan ci gaba da ba da gudummawa wajen tayar da ra'ayin Bandung, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Asiya da na Afirka, da cimma burin bunkasa kasashe masu tasowa tare.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron shugabannin kasashen Asiya da na Afirka. Sin na fatan yin kira da farfado da sabuwar dangantakar abokantaka tsakanin kasashen Asiya da na Afirka bisa manyan tsare tsare, da zurfafa hakikanin hadin gwiwa tsakaninsu, tare da samun babbar nasara a daidai wannan lokaci.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China