A jiya Litinin 20 ga watan nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da firaministan kasar Pakistan Mian Muhammad Nawaz Sharif a birnin Islamabad na kasar Pakistan, inda suka cimma matsaya guda game da dorewar muhimmiyar dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu daga dukkan fannoni, tare da bukatar raya hadin kan su, da kuma kokarin sada zumunta a tsakaninsu.
Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana wasu shawarwari 5, game da raya dangantakar dake tsakanin Sin da Pakistan.
Na farko, ya ce, ya wajaba a kiyaye mu'amala a tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu, da ba da jagoranci ga aikin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da sa kaimi ga gwamnatoci, da hukumomin tsara dokoki, da jam'iyyu, da sojojin kasashen biyu wajen tabbatar da gudanar mu'amala da juna. Ya ce, kasar Sin na jinjinawa kasar Pakistan, bisa goyon bayanta ga Sin kan batutuwan yankin Taiwan, da Xinjiang, da Tibet, da tekun kudu da dai sauransu, kana Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga Pakistan wajen tabbatar da ikon mallaka, da cikakken yankin kasar, da kuma karfafa hanyar samun bunkasuwa mai dacewa da halin da ake ciki a kasar.
Na biyu, ya ce, akwai bukatar kara gina zirin tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu, da dora muhimmanci ga gina mashigin teku na Gwadar, da aiwatar da harkokin sufuri, da makamashi, da kuma hadin gwiwar sana'o'in kasashen biyu, don cimma burin samun moriyar juna, da bunkasuwa tare.
Na uku, a kara yin hadin gwiwa a fannin tsaron kasashen biyu. A cewarsa, kasar Sin na yabawa kasar Pakistan, bisa gudummawarta ga yaki da ta'addanci a duniya, da manufar aiwatar da yaki da ta'addanci bisa halin da ake ciki a kasar, kana tana fatan ci gaba da taimakawa Pakistan din wajen inganta karfinta na yaki da ta'addanci.
Na hudu, shugaba Xi ya ce, kamata ya yi a gudanar da bikin sada zumunta tsakanin Sin da Pakistan na shekarar 2015 yadda ya kamata, da kara gudanar da mu'amala a fannonin al'adu, da ba da ilmi, da horar da matasa, da hadin gwiwar kafofin watsa labaru da dai sauransu.
Na biyar, a yi amfani da dandalin MDD, da kungiyar hadin gwiwa ta birnin Shanghai, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu kan manyan batutuwan duniya, kamar batun kwaskwarima ga MDD, da batun sauyin yanayi, da tsaron hatsi, da tsaron makamashi da dai sauransu. (Zainab)