Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta kira taron manema labarai a yau Jumma'a, inda ta fidda bayanai game da ziyarar aiki da shugaban kasar Xi Jinping zai kai kasar Pakistan da Indonesia, inda zai halarci taron shuwagabannin Asiya da Afirka, da kuma bikin tunawar cikon shekaru 60 da taron Bandung.
Yayin da ya ke bayani game da ziyarar shugaba Xi a kasar Indonesia, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Liu Zhenmin, ya ce a halin yanzu, yanayin neman zaman lafiya, da bunkasuwa, da hadin gwiwa, da kuma cimma moriyar juna na ci gaba da yaduwa tsakanin kasashen duniya, don haka ne kuma huldar dake tsakanin kasashen duniya ke ci gaba da zurfafa.
A daya hannun kuma, shugabannin kasashen Asiya da Afirka za su sake saduwa, a yayin bikin cika shekaru 60 da gudanar taron Bandung, inda za su tattauna kan yadda za a ci gaba da gudanar da kudurorin Bandung yadda ya kamata.
Bugu da kari, Liu Zhenmin ya jaddada cewa a tsahon lokaci, kasar Sin na ta habaka hadin gwiwar dake tsakanin ta da kasashen Asiya da na Afirka, kuma taron da shugaba Xi Jinping zai halarta, ya matukar nuna aniyar kasar Sin game da ciyar da hadin gwiwa, da bunkasuwar kasashen Sin da Afirka gaba. (Maryam)