Wata sabuwar kididdiga da ma'aikatar kudin kasar Amurka ta fitar a jiya Litinin, ta nuna cewa kasar Sin ta ci gaba da rage yawan takardun basussukan kasar Amurka da take mallaka, wadanda darajarsu ta ragu da Dala biliyan 5.2 a watan Janairun kadai.
Kididdigar ta nuna cewa wannan ne wata na biyar a jere da kasar ta Sin ke daukar wannan mataki, yayin da Sin din ke ci gaba da kasancewa ta farko a kasashen da ke mallakar takardun basussukan Amurkan a duniya baki daya.
Bisa wannan kididdigar, an ce yawan takardun basussukan kasar Amurka da kasar Sin ke rike da su ya zuwa watan Janairun bana, ya kai dalar Amurkan triliyan 1.2391, adadin da ya yi kasa da na watan Disamban bara, wato dala trillion 1.2386.
Game da wannan mataki, gwamnatin kasar Sin ta bayyana cewa kasuwar takardun basussukan Amurka, wata muhimmiyar kasuwa ce gare ta. Kuma kara yawan takardun ko rage adadinsu, harka ce ta yau da kullum a fannin zuba jari. Don haka kasar Sin za ta ci gaba da daidaita, da kuma kyautata wannan aiki bisa sauyawar yanayin kasuwa.(Kande Gao)