Rundunar sojojin Sudan ta Kudu ta sanar a ranar Litinin cewa, ta bindige har lahira 'yan tawaye 130 a yayin gumurzu a 'yan kwanaki na baya bayan nan a jihar Upper Nile.
Wadannan mayaka na karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar, in ji Philip Aguer, kakakin rundunar sojojin Sudan ta Kudu a cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Dakarun 'yan tawaye dake karkashin Riek Machar sun kai hare hare kan sansanonin sojojin 'yantar da al'ummar Sudan SPLA a kewayen birnin Renk da ke jihar Upper Nile, inda kuma sojojin suka yi gumurzu da su, kuma bayan kwanaki biyu ana gumurzun, mun samu galaba kansu, in ji mista Aguer.
Kakakin ya kuma bayyana cewa, sojojin SPLA goma sha hudu aka kashe tare da jikkata wasu goma sha bakwai a yayin wannan gumurzu. (Maman Ada)