in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNMISS ta yi tir da shiga harabarta a Bentiu
2015-03-18 10:12:19 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya a kasar Sudan ta Kudu UNMISS da kakkausar murya ta yi suka ga abin da ta kira take 'yancin ba da kariya ga fararen hula da sojojin 'yan tawaye suka yi a sansaninta dake Bentiu na jihar Unity, tana mai kira ga dukkan bangarorin dake fada da juna da su guji aiwatar da ayyukan da za su lalata kariya a yankunan fararen hula.

UNMISS ta ce, ta damu matuka game da fadan da ya faru a safiyar ranar ta Talata, da kuma yammacin rana a harabar da sansaninta yake a Bentiu dake jihar Unity, da suka hada da fada da motocin harba manyan makaman da ya fado a harabar da fararen hula suke.

Kamar yadda mukaddashin kakakin majalissar Farhan Haq, ya yi bayani ya ce, tawagar ta yi suka da kakkausar murya a kan saba yarjejeniyar kariyar harabar fararen hula da sojojin 'yan tawaye na SPLA suka yi. A yanzu haka tawagar UNMISS na ba da kariya ga fararen hula 53,000 a Bentiu.

A cewar tawagar, fada a wuraren Renk ya biyo bayan harin da sojojin 'yan tawaye suka kai a makon jiya, a ciki da wajen Wad Dakona, 'yan kilomita kadan daga kudancin Renk. Fada kuma tsakanin wadannan wurare ya haifar da babban martani daga sojoji tun lokacin da yarjejeniyar zaman lafiyar ta ruguje a farkon wannan watan. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China