A yayin da ranar kammala shawarwarin zaman lafiya na Sudan ta Kudu ke kusantowa, shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar sun gana a ranar Talata a birnin Addis Abeba na kasar Habasha bisa shirin shawarwari a karkashin shiga tsakanin kungiyar IGAD.
Zagayen karshe na tattaunawar zaman lafiya na Sudan ta Kudu, an kaddamar da shi a ranar 23 ga watan Febrairu a karkashin shiga tsakanin kungiyar gabashin nahiyar Afrika IGAD, bisa burin kawo karshen yaki na fiye da shekara guda a kasar.
Kungiyar IGAD ita ce dai ke kulawa da shiga tsakani na shawarwarin Sudan ta Kudu, ta yadda za'a cimma mafita kan rikicin da ke shafar wannan kasa tun cikin watan Disamban shekarar 2013. Bangarorin dake rikici da juna sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin tsagaita bude wuta domin kawo karshen tashin hankalin zubar da jini a kasar Sudan ta Kudu, duk yawan take yarjejeniyoyin tsagaita bude wuta. Mista Kiir da Machar sun rattaba hannu a ranar 1 ga watan Febrairu kan wata sabuwar yarjejeniya domin kammala matakin karshe na shawarwarin kafin ranar 5 ga watan Maris, tare da batun kafa wata gwamnatin hadaka domin tabbatar da rikon kwarya nan da ranar 9 ga watan Julin wannan shekarar. (Maman Ada)