Wakilan bangarori biyu masu adawa da juna a Sudan ta Kudu, na ci gaba da tattaunawa karkashin kulawar kungiyar shuwagabannin kasashen gabashin Afirka ta IGAD.
Rahotanni sun bayyana cewa, za a ci gaba da zantawa tsakanin wakilan sassan biyu a Juma'ar nan, duk kuwa da kammalar wa'adin karshe na tattaunawar a jiya Alhamis.
Shugaba Salva Kiir da tsahon mataimakinsa, wanda kuma ke jagorantar bangaren 'yan tawayen kasar sun rattaba hannu, kan yarjejeniyar karshe ne a ranar 1 ga watan Fabarairu, aka kuma sanya ran 5 ga watan Maris ta zama ranar kammmala tattaunawar karshe. Tattaunawar da aka yi fatan za ta ba da damar kafa gwamnatin hadaka ta rikon kwaryar kasar, kafin 9 ga watan Yulin dake tafe.
Da yake tsokaci game da ci gaban da aka samu, wakilin kungiyar ta IGAD game da Sudan ta Kudu Seyoum Mesfin, ya ce, shugaba Kiir da Dr. Machar sun gana gaba-da-gaba, za kuma su ci gaba da tattaunawa a Juma'ar nan. Daga nan sai ya yi kira gare su, da su yi cikakken amfani da lokacin da ya rage wajen tabbatar da cimma nasarar da ake fata.
Mr. Mesfin ya ce, batun tsaro da na rabon iko, da kuma tsare tsaren harkokin gudanar da mulki, su ne suka rage cikin batutuwan da ake fatan cimma daidaito a kan su. (Saminu)