A ranar 6 ga wata, shugabannin bangarorin biyu na Sudan ta Kudu ba su kai ga rattaba hannu kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya ta karshe ba, a don haka, yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar ya sake samun tsaiko. Shugaban kungiyar gwamnatocin gabashin Afrika"IGAD", kuma firaministan kasar Habasha, Hailemariam Dessalegn ya ba da sanarwar, inda ya bayyana bakin cikinsa kan sakamakon da aka samu.
A game da wannan batu, Hong Lei ya ce, kamata ya yi kasa da kasa su ci gaba da nuna goyon baya ga kokarin kungiyar "IGAD" na shiga tsakani. Kuma kasar Sin na fatan ci gaba da yin mu'amala da kungiyar da kuma sauran hukumomin dake kokarin shiga tsakani kan wannan batu, a kokarin sa kaimi ga daidaita batun Sudan ta Kudu tun da wuri.(Fatima)