A jiya Talata ne kwamitin sulhun MDD ya zartas da wani kuduri, wanda ya tanaji kakaba takunkumi ga dukkanin wadanda ke da nufin kawo cikas, ga yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu.
Takunkumin dai ya kunshi hana irin wadannan mutane fita zuwa kasashen waje, da kuma daskarar da jarinsu. Kaza lika kudurin ya nuna aniyar kwamitin sulhun na mai da hankali kwarai ga kisan mutane, baya ga wadanda ke samun raunuka sakamakon tashe tashen hankula a Sudan ta Kudun.
Ya ce mutane kimanin miliyan 2 ne suka rasa gidajensu a sakamakon musayar wuta tsakanin sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu, da mayakan kungiyar 'yan adawar kasar, tsakanin watan Disambar shekarar 2013 zuwa yanzu.
Don haka kwamitin sulhun ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar Sudan ta Kudun, da su aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla, su kuma dukufa wajen cimma matsaya guda, game da cikakkiyar yarjejeniyar.
Bisa wannan kuduri, kwamitin sulhun MDDr ya yanke shawarar sanya takunkumin hana zirga zirga zuwa ketare, da daskarar da jarin masu yiwa shirin shimfida zaman lafiyar kasar kafar ungulu. Cikin wadanda takunkumin zai shafa dai hadda masu kaiwa fararen hula farmaki, da masu sanya yara kanana cikin ayyukan soji.
Bugu da kari kudurin ya nuna cewa, kamata ya yi nan da shekara daya, dukkanin kasashe mambobin MDDr su dauki matakan da suka wajaba, na hana irin wadannan mutane shiga kasashen su, tare da daskarar da jarinsu.
A wani ci gaban kuma, yayin taron da kwamitin sulhun MDDr ya shirya a wannan rana, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana cewa, a halin yanzu, bangarori biyu na kasar Sudan ta Kudu suna gudanar da shawarwarin siyasa a kasar Habasha, karkashin sanya idon wakilan kungiyar IGAD.
Mr. Liu ya ce kasar Sin ta na goyon bayan kwamitin sulhun MDD, game da rawar da yake takawa cikin yakini, kuma za ta taimakawa kungiyar IGAD wajen aikin shiga tsakani.
Tuni dai kwamitin sulhun ya zartas da kuduri mai lamba 2206, domin karfafa gwiwar kungiyar ta IGAD, a kokarin ta na cimma nasarar shawarwarin.
Game da hakan wakilin na kasar Sin ya ce kasar sa na marba da shawarwarin da bangarori biyu na kasar Sudan ta Kudu ke gudanarwa bisa shirin kungiyar IGAD. Haka zalika Sin na fatan bangarorin biyu za su cimma matsaya guda, game da batutuwan da ba a kai ga cimma matsaya kan su ba, a wani mataki na farfado da zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudun, matakin da ya dace da dawamammiyar moriyar jama'ar kasar Sudan ta Kudun.(Lami)