A yayin ganawarsu, Xi Jinping ya bayyana cewa, shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 40 da kulla dangantakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da Turai, kasar Sin tana son ci gaba da shawarwarin manyan jami'an kasashen Sin da Turai, don haka ya kamata a karfafa hadin gwiwar bangarorin biyu yadda ya kamata, domin ciyar da dangantakar abokantaka dake tsakanin Sin da Turai gaba bisa fannoni guda hudu da suka hada da zaman lafiya, ci gaba, yin gyare-gyare da kuma al'adu.
Bugu da kari, ya ce, kasar Sin ta shirya ayyukanta na shekarar 2015 bisa fannoni daban daban yayin manyan taruka biyu da aka kammala ba da dade ba, kana kasar za ta ci gaba da tsara shirinta na raya kasa daga shekarar 2016 zuwa 2020, kuma kasar ta yi imani cewa, bisa shirin za a bullo da sabbin hanyoyi kan hadin gwiwar Sin da Turai.
A nasa bangaren, Martin Schulz ya bayyana cewa, Turai na son hada kai da kasar Sin domin karfafa hadin gwiwar bangarorin biyu bisa fannoni daban daban yadda ya kamata, da kuma inganta dangantakar abokantaka dake tsakanin sassan biyu bisa fannoni guda hudu. (Maryam)