in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara gudanar da taron koli na hudu na Kungiyar tarayyar Turai a Brussels
2014-04-03 10:54:48 cri
A jiya Laraba ne aka fara gudanar da taron koli na hudu tsakanin kungiyar tarayyar Turai da kasashen Africa a Brussels. Taron mai taken "saka jari a kan fasahar jama'a, samar da yalwar arziki da zaman lafiya" na da niyyar kara habaka huldar gamayya tsakanin kasashen dake nahiyoyin Turai da na Africa.

A yayin da yake jawabi a yayin bude taron a karo na hudu a kan Africa da Turai, shugaban kungiyar tarrayya Turai, Von Rompuy ya nuna jin dadinsa game da kimar hulda dake tsakanin Africa da kungiyar tarayyar ta Turai, tare da bayyana muradin kungiyar na ganin an inganta gaba dayan wannan hulda tsakanin Africa da Turai.

Kamar dai yadda agendar taron ta bayyyana za'a duba halin da ake ciki a Jamhuriyar Africa ta tsakkiya tare da duba sabuwar manufa na bunkasa cinikayya tsakanin kasashe tare kuma da daukar mataki a kan canjin yanayi na duniya. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China