Bisa labarin da aka bayar, an ce, a ranar 9 ga wata, majalisar dokokin Turai ta zartas da wani kudurin dake shafar kulla huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kungiyar EU da yankin Taiwan, kuma ta yi kira ga kwamitin kungiyar EU da ya kaddamar da yin shawarwari da yankin Taiwan kan yarjejeniyar ba da tabbaci ga zuba jari da shiga kasuwannin juna, a kokarin zurfafa dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin bangarorin biyu.
Game da lamarin, madam Hua ta bayyana cewa, kasar Sin ba za ta nuna bambancin ra'ayi kan kulla huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin jama'ar yankin Taiwan da na kasashen kungiyar EU ba, amma ta ki amincewa da a raya irin wannan hulda tsakanin hukumominsu. Tana fatan majalisar dokokin Turai za ta tsaya tsayin daka kan bin manufar kasar Sin daya tak a duniya, da yin taka-tsamtsam wajen daidaita batutuwan dake shafar yankin Taiwan, da daina ma'amala da hukumomin yankin Taiwan da kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar cinikayya tsakaninta da hukumomin yankin Taiwan. Da fatan majalisar dokokin Turai za ta yi kokarin kyautata dangantaka tsakaninta da kasar Sin a nan gaba.(Fatima)