Shugaban tawagar kasar Sin Chen Shiqiu ya ba da wani jawabi a yayin taron, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta nuna goyon baya da a mutunta bambancin dake tsakanin kabilu daban daban, addinai daban daban da kuma al'adu daban daban, kuma tana fatan samun zaman lumana tsakanin kabilu daban daban da masu bin addinai daban daban na Asiya da Turai, ta yadda za a iya karfafa zaman lafiya da zaman karko na yankin.
Mr. Chen ya kara da cewa, ya kamata mambobin taron Asiya da Turai su bi ka'idojin girmama juna, nuna adalci da kuma nuna fahimtar juna, karfafa mu'amalar dake tsakanin al'adu daban daban da addinai daban daban cikin himma da kwazo, domin ciyar da fahimtar junansu gaba, ta yadda za a iyar karfafa hadin gwiwa tare da kuma ba da gudumawa yadda ya kamata wajen kiyaye zaman lafiya, zaman karko da kuma dauwamammen ci gaban yankin Asiya da Turai, har ma na kasa da kasa. (Maryam)