Firaministan kasar Sin Li Keqiang da uwar gidansa Cheng Hong sun sauka a filin jiragen sama na Heathrow dake birnin Landan na kasar Ingila, domin fara ziyarar aiki bisa gayyatar firaministan kasar David Cameroon.
A yayin wannan ziyara, Li Keqiang zai gana da sarauniyar Ingila Elizabeth II, tare da gudanar da shawarwari da firaministan kasar David Cameron, kana zai yi jawabi gaban kungiyar masana mafi tasiri a kasar ta Ingila.
Bugu da kari Mr. Li zai halarci taron tattaunawa kan tattalin arzikin duniya tsakanin Sin da Ingila, da dandalin tattaunawa kan hada-hadar kudi na kasashen biyu, sa'an nan zai gana da walikan ma'aikata da 'yan kasuwa na kasashen biyu dake kasar ta Ingila. (Zainab)