Bayan karbar takardun aikin, shugaba Hassan Sheikh Mohamud, ya yi shawarwari tare da jakadun biyar, inda ya bayyana cewa, lamarin farfado da dangantakar diflomasiyya tsakanin kasarsa da kasashen Turan 5, ya nuna a fili, irin amincewar da gamayyar kasa da kasa ke yi, ga yunkurin gwamnatinsa ta fuskar samar da ci gaba, shugaban ya kuma ba da tabbacin ba da dukkanin gudumawa ga harkokin ci gaban duniya.
A jawabinsa jakadan kasar Faransa a Somaliya cewa ya yi, lamarin farfadowar huldar difliomasiyya wani babban ci gaba ne da aka samu, don gane da dangantakar kasashen biyu, domin kuwa cikin shekaru 20 da suka gabata, kasar ta Faransa ba ta taba aikewa da jakada zuwa kasar Somali ba, amma a halin yanzu, kasashen biyu za su farfado da dangantakar aminci tsakaninsu, kan fannonin daban daban da suka hada da siyasa, da tsaro, da ci gaba da dai sauransu. (Maryam)