in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Turai da Amurka sun fidda sabbin matakan kakabawa Rasha takunkumi
2014-09-12 14:31:10 cri
A jiya Alhamis ne shugaban majalissar gudanarwar tarayyar turai Herman Van Rompuy ya fidda wata sanarwa dake cewa, sabon shirin kakabawa Rasha takunkumi da kungiyar tarayyar kasashen Turai ta (EU) ta shirya aiwatarwa zai fara aiki a Juma'ar nan.

Kaza lika sauran batutuwan dake kunshe cikin kundin majalisar sun fayyace cewa, akwai bukatar kayyade jarin da Rasha za ta zuba a hada-hadar kasuwannin Turai. Kana akwai batun hana fitar da kayayyakin aiki da na fasahohin soja zuwa kasar ta Rasha. A sa'i daya kuma, za a kara sunan wasu mutane 24 da takunkumin zai hana damar shiga kasashen Turai, tare da daskarad da kadarorin su dake turan. Matakin da zai sanya yawan mutane da takunkumin ya shafa kaiwa mutum 119.

Hakan dai na zuwa ne yayin da shi ma shugaba Barack Obama na Amurka ya fidda wata sanarwar ta daban, dake cewa za a kara fadada takunkumin da aka sanyawa Rasha a fannonin hada hadar kudi, da makamashi, da tsaron kasa da ma wasu karin muhimman sassa.

Dadin dadawa, shugaba Obama ya ce matakin da kasar ta sa ke dauka, tamkar martani ne ga Rashan, don gane da ayyukan da take gudanarwa na keta doka a kasar Ukraine.

Bisa sabon shirin dai ana fatan kara rage bunkasuwar tattalin arzikin Rasha, tare da mai da ita saniyar ware a fannin siyasa. Kana ana fatan gabatar da hakikanin abubuwan dake cikin kundin bayanan a juma'ar Juma'ar nan.

Sai dai game da wannan batu na karin takunkumi ga Rasha, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Alexander Lukashevich, ya bayyana cewa ci gaba da kakaba takunkumi ga Rasha da kungiyar EU ke yi ba shi da ma'ana, kuma bai dace da moriyar EUn ba. Ya ce Rasha ta riga ta nanata cewa a shirye take ta mai da martani. Har wa yau ta nuna rashin amincewar ta da duk wani matakin sanya takunkumi da Amurka ke dauka a kan ta.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China