An rufe taron shugabannin nahiyoyin Asiya da Turai karo na 10 a birnin Milan a ran 17 ga wata, wanda ke da zummar karfafa mu'ammala tsakanin Asiya da Turai da sa kaimi ga hadin gwiwa ta fuskar hada-hadar kudi da tattalin arziki.
A gun bikin rufe taron, shugaban kwamitin gudanarwa na tarayyar Turai Herman Van Rompuy ya ce, shugabannin da suka halarci wannan taro sun kai ga matsaya daya, inda suka yarda da su dauki matakai daga dukkan fannoni domin yaki da manufar ba da kariya da kawar da kunci iri na ciniki da ake yi da ba na haraji ba da dai sarausu.
Taron na kwanaki biyu da ya gudana a karkashin jagorancin firaministan kasar ta Italiya Matteo Renzi, ya samu halartar shugabannin kasashe 50 da kungiyoyin kasa da kasa daga nahiyoyin Asiya da Turai. (Amina)