in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Congo-Kinshasa ya gana da ministan harkokin wajen Sin
2015-01-17 17:21:56 cri
Shugaban kasar Congo Josef Kabila, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, a birnin Kinshasa fadar mulkin kasar, yayin ziyarar aiki da Mr. Wang din ya gudanar a jiya Juma'a.

Cikin jawabin da ya gabatar Mr. Kabila ya bayyana cewa, kasar Congo-kinshasa na mai da hankali sosai kan matsayin kasar Sin cikin harkokin kasa da kasa, tana kuma godiya kwarai dangane da taimako, da goyon bayan da kasarta Sin ke baiwa kasarsa, a fannonin bunkasar tattalin arziki, da ikon mulki, da kuma cikakken ikon kiyaye yankunan kasar.

Shugaba Kabila ya yi fatan karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban, da kuma kara fahimtar juna cikin harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

A nasa bangare Wang Yi ya ce, kasar Sin na fatan karfafa hadin gwiwa da Congo-Kinshasa, ta yadda dangantakar hadin gwiwa ta goyon bayan juna kan harkokin siyasa za ta bunkasa, a kuma kai ga cimma moriyar juna a fannin tattalin arziki, da kuma inganta hadin gwiwa a fannin ayyukan tsaro tsakanin Sin da kasar ta Congo-Kinshasa.

Bugu da kari, Wang Yi ya ce, kasar Sin ta amince da hanyar da kasar Congon-Kinshasa ke bi wajen neman bunkasuwa, hanyar ta dace da halin da kasar take ciki. Ya ce kasar Congo-Kinshasa aminiyar Sin ce a nahiyar Afirka, don haka ta ke burin ganin ci gaban hadin gwiwa yadda ya kamata, tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China