in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Congo Kinshasa ya gana da ministan harkokin wajen Sin
2015-01-16 10:46:05 cri
Firaministan kasar Congo Kinshasa Matata Ponyo, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, wanda ke ziyarar aiki a kasar.

A yayin ganawar tasu a jiya Alhamis, Ponyo ya bayyana cewa Congo Kinshasa tana cikin wani muhimmin lokacin na bunkasa, kuma gwamnatin kasar mai ci, na ci gaba da kokarin shimfida yanayin zaman lafiya, da bunkasar tattalin arziki, da gudanar da kwaskwarima, don cimma burin ta na kasancewa sabuwar kasa mafi samun bunkasar tattalin arziki nan da shekarar 2030.

Har wa yau Ponyo ya bayyana aniyar kasar ta kara azama wajen karfafa dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, da yabawa kasar ta Sin, bisa gudummawar da take baiwa Congo Kinshasa, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa.

Ya ce kasar Sin ta cancanci yabo bisa kokarin da ta yi na samun bunkasuwa cikin sauri. Yayin da a hannu guda kasarsa ke fatan yin koyi daga fasahohin kasar Sin, tare da fatan Sin za ta taimakawa Congon wajen cimma wannan buri, musamman a fannin hadin gwiwa a fannonin aikin gona da raya masana'antu.

A nasa bangare, Wang Yi ya bayyana cewa, Congo Kinshasa abokiyar hadin gwiwa ce ga kasar Sin, kuma za ta ci gaba da raya dangantakar abokantaka da kasar Congo Kinshasa a nan gaba, tare da tabbatar da cimma moriyar juna da samun bunkasuwa tare. Haka zalika kasar Sin na goyon bayan kasar Congo Kinshasa, a burin ta na neman bunkasuwa bisa hali da take ciki, za kuma ta kara fadada mu'amala, da hadin gwiwa tsakaninta da kasar Congo Kinshasa wajen gudanar da harkokin kasa, da more fasahohin bunkasuwa.

A wani ci gaban kuma, Mr. Wang Yi ya gudanar da shawarwari tare da takwaransa na kasar Congo Kinshasa Raymond Tshibanda. Inda bayan tattaunawar tasu, ministocin biyu suka gana da 'yan jarida.

Da yake tsokaci yayin zantawar sa da manema labarun, Wang Yi ya bayyana cewa, samun bunkasuwa shi ne tushen warware dukkan matsalolin kasashe masu tasowa, ciki hadda kasar Sin da ma sauran kasashen Afirka.

Mr. Wang ya kara da cewa kasashen Afirka ciki har da kasar Congo Kinshasa, na kokarin neman bunkasa mansana'antu, da zamanantar da kasa. Kana ita ma kasar Sin na gaggauta canja tsarin sana'o'in ta, da fitar da kayayyakin da ake samarwa, kuma tana fatan hada burin samun bunkasuwa na kasashen Afirka, da burin samun ci gaba nata na gida.

Ya ce kari kan hakan, burin kasar Sin ne ta kara samarwa kasashen Afirka taimakon na bunkasa masana'antu, da zamanantar da kasa. Har ila yau Sin na fatan hada kai da kasashen Afirka a fannin sada zumunta, da fadada bunkasuwa tare, da musayar harkokin hidima, da kare halittun nahiyar Afirka, zuwa batun bunkasa tattalin arzikin nahiyar, da ma sauran abubuwan dake da amfani ga jama'ar Afirka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China