in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi tir da kai wa jirgin MONUSCO hari a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo
2013-10-19 16:45:24 cri
Jagoran tawagar MDD ta MONUSCO a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo Martin Kobler da wakiliyar musamman ta MDD a yankin manyan tafkunan Afirka Mary Robinson sun yi tir da harin da dakarun kungiyar M23 suka kaiwa wani jirgin sama mai saukar ungulu, mallakar tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kusa da birnin Goma dake Arewacin Kivu.

Jami'an Biyu sun bayyana harin da dakarun na M23 suka kaddamar ga jirgin wanda ba ya dauke da makaman yaki, dake tsaka da gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a matsayin wani mummunan aiki da sam bai dace ba.

Da yake karin haske dongane da aukuwar wannan lamari, mai magana da yawun MDD Martin Nesirky cewa ya yi wannan ne karo na Biyu cikin mako guda da dakarun kungiyar ta M23 suka kaddamar da makamancin wannan hari. Sai dai ya tabbatar da cewa, mutanen dake cikin jirgin sun tsira da rayukansu, kuma harin bai lahanta jirgin ba.

Tuni dai jagoran tawagar MDD ta MONUSCO Martin Kobler ya jaddada aniyar ci gaba da gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a yankunan jamhuriyar dimokaradiyyar Congon, ciki had da zirga-zirgar jirage masu saukar ungulu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China