in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai kyakkyawar makoma game da hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka
2014-06-10 15:31:42 cri
Shugaban jamhuriyyar dimokaradiyyar Congo Denis Sassou Nguesso, ya bayyana wa 'yan jaridun kamfanin dillancin labaru na Xinhua a birnin Brazzaville cewa, kasar Sin da kasashen Afirka suna bukatar juna a fannonin da suke da kwarewa, tare da kyakkyawar makoma kan hadin gwiwarsu.

Sassou ya bayyana cewa, nahiyar Afirka tana da albarkatun halittu da kwadago, baya ga bunkasuwar tattalin arziki da nahiyar ke samu. Kaza lika kasar Sin tana da fasahohi da fifiko a fagen bunkasuwa.

Shugaban jamhuriyyar dimokaradiyyar Congo ya ce ya yi imanin cewa, za a samu kyakkyawar makoma idan har kasar Sin, da kasashen Afirka suka ci gaba da yin hadin gwiwa.

Game da zabar birnin Shanghai da lardin Guangdong, a matsayin zangon kai ziyara, yayin da ya sauka kasar Sin, Sassou ya bayyana cewa, birnin Shanghai, da lardin Guangdong na da yankuna masu ci gaban tattalin arziki a kasar Sin, kuma kasarsa tana kokarin bunkasa yankin ta ta fuskar tattalin arziki.

Ya ce dalilin ziyarar sa a yankunan biyu shi ne, nazartar fasahohin Sin da kuma neman hadin gwiwa da kasar ta Sin.

Haka zalika, Sassou ya ce, cimma moriyar juna shi ne tushen hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, kana tushe ne na zurfafa hadin gwiwar sassan biyu. A ganinsa, kasashen biyu za su iya yin hadin gwiwa a fannonin aikin gona, da yawon shakatawa, hakar ma'adinai da dai sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China