in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata kasashen Afirka dake yankin Great Lakes su hada kansu, in ji wakilin Sin
2014-08-08 16:21:49 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana a ran 7 ga wata a hedkwatar MDD dake birnin New York cewa, ya kamata kasashen Afrika dake yankin Great Lakes su tsaya tsayin daka wajen yin hadin gwiwa kan harkokin tsaro, da neman samun ci gaba tare don samun nasara gaba daya, a kokarin kara azama ga samun dauwamammen zaman lafiya, da kwanciyar hankali da kuma ci gaba a yankin.

Mr. Liu ya bayyana haka ne a yayin taron kwamitin sulhu na MDD da aka yi kan yanayin da ake ciki a kasar Congo-Kinshasa da batun yankin Great Lakes a wannan rana, inda ya kuma kara da cewa, tun farkon wannan shekara, ana ta samun kyautatuwa kan yanayin da ake ciki a gabashin kasar Congo-Kinshasa, inda ake kokarin aiwatar da tsarin samar da zaman lafiya, tsaro da hadin gwiwa a tsakanin kasar Congo-Kinshasa da yankin Great Lakes yadda ya kamata. Sakamakon haka kasar Sin ta yaba matuka ga kokarin da MDD, gamayyar kasa da kasa, kungiyar tarayyar kasashen Afirka, da kuma taron yankin Great Lakes na Afirka suka yi kan wannan aiki.

Mr. Liu ya ce, a halin yanzu, ana cikin kyakkyawan yanayin wajen kawo karshen tashen hankali a yankin na Great Lakes, don haka ya kamata gamayyar kasa da kasa su ba da taimako kan lamarin ta fannoni guda uku, ta yadda za a iya ciyar da ayyukan shimfida zaman lafiya, zaman karko da kuma bunkasuwar yankin cikin dogon lokaci gaba. Da farko, ya kamata a kiyaya yanayin tsaro cikin hadin gwiwa, sa'an nan, a samu bunkasuwa cikin hadin gwiwa, domin jama'ar yankin su smu alheri, a karshe dai kuma, ya kamata a tsaya tsayin daka kan cimma moriyar juna cikin hadin gwiwa.

Bugu da kari, Mr. Liu ya kara da cewa, kasar Sin ta mai da hankali sosai kan bunkasa dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka, kuma tana tsayawa daukar ra'ayi na goyon bayan kasashen Afirka wajen warware matsalolinsu da kansu. Haka kuma, kasar Sin za ta aiwatar da "Sanarwar kulla abokantakar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka don kiyaye zaman lafiya da tsaro", a kokarin tallafawa Afirka a fannin kafa tsarin tsaron nahiyar baki daya. A sa'i daya kuma, kasar Sin za ta ci gaba da hadin gwiwa tare da gamayyar kasa da kasa don ba da gudummawarta ta fuskar neman samun zaman lafiya, da kwanciyar hankali da kuma wadata a nahiyar Afirka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China