Shugaban kasar Congo Denis Sassou Nguesso ya yi kira a ranar Litinin ga gamayyar kasa da kasa da ta karfafa hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci dake kawo barazana sosai ga zaman lafiya da tsaro a duniya. Shugaba Sassou Nguesso ya yi wannan kira a yayin bikin gabatar da sakon taya murnar sabuwar shekarar 2015 tare da jami'an diplomasiyya da kananan jakadun kasashen waje dake kasar.
Karuwar ta'addanci na kasancewa wata babbar barazana kai tsaye ga zaman lafiya, tsaron jama'a baki daya. Munanan ayyuka da tashe tashen hankalin da kungiyoyin ta'addanci ke aikata a ko'ina cikin duniya suna karya lagon kasashenmu da kuma gurgunta kokarinmu na neman ci gaba, in ji shugaban kasar Congo. (Maman Ada)