in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawaga ta 17 ta sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin dake Congo Kinshasa ta kammala mika ayyukanta ga tawaga ta 18
2014-12-25 15:00:58 cri
A ranar Talata ne tawaga ta 17 ta sojojin kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin dake Congo Kinshasa ta kammala mika ayyukanta ga tawaga ta 18 a sansanin kasar Sin na birnin Bukavu dake jihar kudancin Kivu.

Tawaga za ta kwashe watanni 8 tana gudanar da ayyukan bincike kan aikin gina hanyoyin motoci da filayen jiragen sama da dai sauransu, kana reshen likitoci na tawagar zai rika kula da lafiyar rukunoni 20 na jihar kudancin Kivu na tawagar MDD ta musamman dake kasar Congo Kinshasa da ma'aikatansu.

Shugaban reshen sojojin injiniyoyi na tawagar Sin ta 18 Gan Wei ya yi bayani cewa, a wannan karo, an mika na'urori da kayayyaki da kudi da kuma takardu masu amfani, kana an mika fasahohi da ayyuka, da sanar da halin da ake ciki, da kuma yin mu'amala a fannin tunani, daga tawaga ta 17 zuwa ta 18 da tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China