in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakiyar faraministan Sin ta gana da shugaban jamhuriyar Congo
2014-06-19 10:15:47 cri

Mataimakiyar faraministan kasar Sin, madam Liu Yandong ta gana a ranar Laraba da shugaban kasar Congo, Denis Sassou-Nguesso, inda jami'an biyu suka jaddada niyyar kara zurfafa huldar dangantaka tsakanin kasashen biyu ta fuskar ilimi, al'adu da fasaha.

Kasar Sin da Afrika, kowanensu na da dogon tarihi da arzikin al'adu, kuma jamhuriyar Congo ta cigaba da kasancewa a sahun gaba wajen musanyar al'adu, da kuma kan dangantaka tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afrika, in ji madam Liu a yayin babban dandalin shekara shekara kan al'adun duniya a birnin Shanghai.

Mataimakiyar faraministan kasar Sin ta jaddada niyyar cigaba da fadada hulda, tare da jamhuriyar Congo domin bunkasa musanya da karfafa dankon zumunci dake tsakanin kasashen biyu.

Haka kuma kasar Sin, a shirye take wajen ciyar da huldar dangantaka cikin karko, in ji madam Liu.

Bisa nuna yabo kan karfin abokantakar dake tsakanin kasashen biyu, shugaba Sassou-Nguesso ya bayyana cewa, kasar Congo na fatan kara cigaba da karfafa hadin kai tare da kasar Sin domin kara samun bunkasuwa bisa tushen huldar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China