Za a yi bikin ranar bunkasa masana'antu ta Afirka ta shekarar 2014 a Congo Kinshasa
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Congo Kinshasa wato ACP ya bayar, an ce, a ranar Alhamis 20 ga wata za a gudanar da bikin ranar bunkasa masana'antu ta Afirka ta shekarar 2014 a birnin Kinshasa na kasar, inda wakilan hukumomin MDD da abin ya shafa, masanan ilmin masana'antu na kasashen Afirka, masana harkokin tattalin arzikin masana'antu, malaman jami'o'i da sauransu za su halarci bikin tare da tattauna makoma da yanayin ci gaban masana'antun Afirka.
A shekarar 1989 ne, babban taron MDD ya tsaida ranar 20 ga watan Nuwanban kowace shekara a matsayin ranar bunkasa masana'antu ta Afirka da nufin sa kaimi ga kasa da kasa da su taimaka wajen bunkasa masana'antu a nahiyar Afirka. (Zainab)