in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na goyon bayan kare albarkatun muhalli a Congo
2014-11-25 13:34:55 cri

Jakadan kasar Sin dake Congo, Guan Jian ya bayyana a ranar Litinin cewa, gwamnatin Sin za ta bayar da taimakon dalar Amurka dubu dari daya domin tallafawa gandun namun dajin kasa na Odzala-Nkokoua dake arewa maso yammacin kasar.

Jami'in diplomasiyar kasar ya yi wannan sanarwa bayan cimma sanya hannu kan wata yarjejeniya tare da gandun namun dajin kasa na Odzala-Kokoua. Bisa wannan yarjejeniya, wannan tallafin kudi zai taimaka wajen gina hanyar mota da ta hada sabon sansanin gandun daga bangarensa na gabashi zuwa babbar hanyar kasa lamba ta biyu, da kuma bangare gudan har zuwa tafkin Mambili. Wannan gudunmuwar kudin na da manufar tallafawa kiyaye muraba'in kilomita dubu 13 da dari 5 na dajin kasar dake kunshe da gandun namun dajin Odzala-Kokoua, hakan ya bayyana niyyar kasa da kasa da gwamnatin kasar Sin ta dauka a cikin kare mullahi da kuma bunkasa ci gaban karko na Afrika, in ji mista Guan.

Makasudin shi ne na kiyaye albarkatun muhalli da albarkatun halittun na wannan gadun dajin dake kunshe da kwatarniyar Congo, babban yankin albarkatun muhalli na duniya bayan dajin Amazoniya dake Latin Amurka, da kuma ba da damar yaki da ayyukan dake da nasaba da farautar namun daji ba bisa doka ba, da fataucin namun dajin da ake kiyaye, musammun ma giwaye. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China