Kakakin gwamnatin kasar ya bayyana cewa, wasu dakaru sun yi yunkurin kwace wannan sansanin soja a wannan rana. Kuma wani jami'in tsaro na kasar ya ce, bangaren sojan kasar ya kama masu kai harin fiye da 20.
Gwamnatin kasar Congo Kinshasa ba ta bayyana ko akwai wadanda suka mutu ko suka raunata a sakamakon harin ba. Bisa labarin da wanda ya gane wa idonsa ya bayar, ya ce, masu kai harin guda 7 da ma'aikatan tsaron kasar biyu sun rasa rayukansu a sakamakon rikicin da ya biyo bayan harin.
Wannan lamari ya haifar da zaman zullumi a birnin Kinshasa, amma al'umma sun daidaita a wannan rana da maraice. (Zainab)