Bisa labarin da jaridar Tribune ta kasar Kamarun ta fitar, ta ce gwajin wanda ya gudana a kwanakin baya, ya bada damar nazartar amfani da fasahar sadarwa ta 4G, domin inganta karfin na'urorin na sa ido a kasar ta Kamaru. Za kuma a kafa na'urorin sa idon kimanin 70 a sassan birane shida da suka hada da Yaounde, da Douala, da Waza da dai sauransu. Kana an ce cikin na'urorin akwai wadanda ka iya daukar bidiyo daga nisan kilomita 5. (Zainab)