in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe a kalla mayakan boko haram 180 inji sojojin kasar Kamaru
2014-12-12 20:57:14 cri
A kalla mayakan boko haram 180 ne aka tabbatar da rundunar tsaron kasar Kamaru da jami'an tsaron dake arewacin kasar suka kasha kamar yadda wani jami'i da ya nemi a sakaya sunan shi daga rundunar sojin ya tabbatar a ranar jumma'an nan.

A cewar wannan jami'i mayakan an kasha su lokacin wani hari da aka kai masu a maboyar su dake Amchide a arewacin kasar dake kan iyaka da Najeriya da misalin karfe 8 na daren alhamis agogon wajen.

Majiyar ya ce kusan mayakan su 400 suka kai hari ma sojojin kamaru da jami'an tsaron kasar a lokacin wannan arangama an kasha mayakan kusan 180 sai dai ba bu wanda ya rasa ransa a bangaren sojojin kasar.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China