Rundunar sojojin ruwa rukuni na 16 na kasar Sin, da takwarorinsu na kasar Kamaru, sun gudanar da atisayen soja a karon farko a gabar tekun Guinea, domin yaki da 'yan fashin teku.
Atisayen na ranar 2 ga wata dai shi ne irinsa na farko da sojojin ruwan kasashen biyu suka gudanar, bisa kudurin inganta kwarewarsu a fannin kiyaye tsaro a kan teku, da tinkarar barazanar laifukan da suka shafi teku.
Yayin atisayen sojin, dakarun kasashen biyu sun daidaita aikin ba da umurni, da na jibge sojoji da kuma jigilar jiragen ruwa.
Kammala atisayen sojin da ya gudana cikin nasara, da jiragen ruwa rukuni na 16 na Sin suka gudanar, ya kawo karshen ziyarar kwanaki 4 da suka kai Kamaru, inda daga nan kuma za su zarce zuwa kasar Angola. Kasar Kamaru ta kasance tasha ta 5 a Afirka, da jiragen ruwan rukuni na 16 na kasar Sin suka kai ziyara, kafin hakan sun ziyarci kasashen Tunisiya, da Senegal, da Kodivwa, da kuma Nijeriya. (Danladi)