A yau Asabar da safe ne ma'aikata Sinawa guda 10 suka isa birnin na Yaounde a cikin wani jirgin sama na musamman da gwamnatin Kamaru ta yi hayarsa.
Jakadan Sin da ke Kamaru Wo Ruidi da wasu jami'an gwamnatin Kamaru ne suka tarbi Sinawan a filin saukar jiragen saman kasar.
Tun da farko ministan sadarwa na kasar Kamaru Issa Tchirimna Bakary ya shaidawa manema labarai cewa, an saki uwargidan mataimakin firaministan kasar Amadou Ali da wasu mutane 16 da aka yi garkuwa da su a watan Yuli.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasar Kamaru ta bayar, ta ce ya zuwa yanzu an mika wa hukumomin Kamaru mutane 27 da aka yi garkuwa da su a baya.
A ranar 16 ga watan Mayu ne dai aka sace Sinawan a wurin da suke aiki a arewacin kasar Kamaru. (Ibrahim)