A cewar Bakary, har yanzu ba a samu wata kungiya da ta dau alhakin harin na ranar Jumma'a ba, sai dai kungiyar Boko Haram dake da sansani a Najeriya, ta kan kai hare-hare makamantan wadannan a arewacin kasar ta Kamaru musamaman a baya bayan nan. Ya ce hukumokin Kamaru za su yi bincike kan bayanan da suka samu kafin su fidda sanarwa kan batun.
Wasu dakarun da ba a san ko su waye ba ne dai suka kai hari harabar wani kamfanin kasar Sin dake arewacin kasar ta Kamaru, lamarin da ya sabbaba jikkatar wani ma'aikaci Basine 1, tare da bacewar wasu ma'aikatan su 10.(Bello Wang)