Gidan telebijin na Kamaru ya ruwaito ministan kiwon lafiya kasar Mama Fouda Andre na cewa, tun daga barkewar annobar ta kwalara, an samu yawanci masu fama da ita a yankin arewacin kasar, musamman a jihar Far North. Ya zuwa ranar Talata ta makon jiya 6 ga watan nan, an gano mutane 1609 da suka kamu da annobar ta kwalara a jihar Far North, a ciki kuma 74 sun rasa rayukansu. A halin yanzu, an gano mutane biyu masu fama da cutar a jihar Littoral dake kudu maso yammacin kasar.
Ana ta samun barkewar cutar ta kwalara a kasar Kamaru a wadannan shekaru, musamman a shekarar 2010 da ta 2011. A lokacin, aka samu barkewar cutar mai tsanani a jihohi da dama, wanda ya sa gwamnatin kasar ta nemi taimako daga hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO da sauran hukumomin duniya. (Zainab)