Ministan harkokin wajen Najeriya Aminu Bashir Wali, ya yi kira ga al'ummomin kasa da kasa da su hada kai a kokarin da ake na yaki da cutar Ebola.
Ministan na Najeriya wanda ya yi wannan kiran yayin da ya ke jawabi a taron jakadu na shekara-shekara a birnin Ankara ya ce, muddin ana bukatar a kawar da wannan cuta, wajibi ne kasashen duniya su ba da goyon baya da hadin kai, maimakon a ware kasashen da suke fama da wannan annoba.
Ya ce, a nata bangaren, Najeriya ta tura ma'aikatan sa kai 500 zuwa yankunan da ke fama da wannan cuta, a kokarin da ake na yakar wannan cuta.
A karshen watan Oktoban shekarar da ta gabata ce hukumar lafiya ta duniya WHO ta wanke Najeriya daga wannan cuta, bayan da aka shafe makonni 6 ba a samu ko da mutum guda da ke dauke da cutar ba tun ranar 31 ga watan Agustan shekarar da ta gabata. (Ibrahim)