Mr. Bambury wanda ya bayyana hakan ga taron manema labaru, bayan kammala ziyarar aiki da ya gudanar a kasashen Guinea, da Laberiya da Saliyo, ya kara da cewa duk da kalubalen dake tattare da wannan gagarumin aiki, ba za a dakata ba, har sai an kai ga kawo karshen yaduwar cutar.
Bamburry wanda ya karbi jagorancin shirin na UNMEER cikin watan Satumbar bara, ya ce kawo wannan lokaci, ana kara samun kyakkyawan sakamako a yakin da ake yi da cutar ta Ebola.
Ya zuwa yanzu shirin na MDD da sauran masu tallafa masa, sun taimakawa kasashen da cutar ta fi addaba, da hanyoyin kebe, tare da baiwa wadanda Ebolan ta kama magunguna. Kazalika an samar da kyakkyawan tsarin binne wadanda cutar ta hallaka.
Ya ce duk da wadannan nasarori, matsalolin da suka hada da fantsamar da cutar ta yi a sassa daban daban, da yadda wasu al'ummomi ke kin baiwa jami'an lafiya hadin kai, na cikin manyan kalubalen da ake fuskanta.
Daga nan sai Mr. Banburry ya bayyana matakan wayar da kan jama'a da sanya ido, tare da kara azamar aikin yaki da cutar, a matsayin matakan da ya wajaba a ci gaba da dauka, a wannan gaba da yaduwar cutar ke ci gaba da raguwa. (SAminu Hassan)