Sabon jagoran shirin yaki da cutar Ebola na MDD a kasar Saliyo Ismail Ould Cheikh Ahmed, ya ce a yanzu haka Saliyo na cikin managarcin yanayin yaki da Ebola, sabanin halin da kasar ta tsinci kanta a baya.
Shugaban shirin na UNMEER ya bayyana hakan ne a jiya Juma'a, cikin jawabinsa na farko ga taron manema labaru.
Ahmed ya ce a halin yanzu, shirin yaki da cutar Ebola a Saliyon ya karkata ga mataki na biyu, mai kunshe da kudurin dakile yaduwar cutar, da kuma tsara cimma nasarar hakan.
Ya ce daya daga ci gaban da aka samu shi ne, a yanzu al'ummar kasar sun kara fahimtar alkaluman yaduwar wannan cuta, duk kuwa da karin masu kamuwa da ita da aka samu a baya bayan nan.
Alkaluma sun nuna cewa kusan mutane 250 ne suka harbu da cutar a makon da ya gabata a kasar ta Saliyo, duk da hakan dai hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce yaduwar cutar na kara raguwa.
A cewar wakilin musamman na WHO David Nabarro, MDD ta tattara karin kudaden yaki da yaduwar cutar, a wani mataki na yunkurin ganin bayan cutar kacokan.
Nabarro ya kara da cewa, da fari MDDr ta bukaci tattara kudade da yawansu ya kai dala biliyan ne a cikin watan Satumba, kafin daga bisani a maida kudaden da ake bukata zuwa dala biliyan 1 da miliyan dari 4 a watan Oktoba.
Wakilin na MDD ya ce cikin wannan adadi, an samu nasarar tattara kudin da suka kai biliyan da miliyan dari daya, wanda hakan ke nuna nasarar da aka cimma wajen samar da babban tallafi a fannin yaki da cutar ta Ebola. (Saminu Alhassan)